
Jharkhand jiha ce, da ke a Gabashin ƙasar Indiya. Tana da yawan fili kimanin kilomita arabba’i 79,710 da yawan jama’a 32,988,134 (in ji ƙidayar shekarar 2011). Jihar tarayyar Indiya ce daga shekara ta 2000. Babban birnin jihar Ranchi ne; birnin mafi girman jihar Jamshedpur ne. Draupadi Murmu shi ne gwamnan jihar. Jihar Jharkhand tana da iyaka da jihohin biyar: Bihar a Arewa, Uttar Pradesh a Arewa maso Yamma, Chhattisgarh a Yamma, Odisha a Kudu da Bengal ta Yamma a Gabas.
Hotuna








8 images
