factograf
HA

Jemage

Jemage
All data from the card 4
Tsatso
bat meat (en)
Tsayi
1 in da 1 ft
Faɗi
6 ft
Audible frequency range
2,000 hertz (mul) — 110,000 hertz (mul)
jemage maƙale akan bishiya
jemage maƙale akan bishiya
jemage yana fira
jemage yana fira
jemagu akan bishiya
jemagu akan bishiya
jemagu da yawa akan bishiya
jemagu da yawa akan bishiya
jemagen sirilanka akan hannu
jemagen sirilanka akan hannu
jemagu suna tashi a sama
jemagu suna tashi a sama
dayigiram ɗin jemagu
dayigiram ɗin jemagu
jemagun indiya
jemagun indiya
8 images

Jemage halitta ce dake a cikin nau'ukan halitta na mammals, wasu na zacin jemage amatsayin tsuntsu, amma ba'a dangin tsuntsaye yake ba. Jemage na daya daga cikin dabbobi masu shayarwa na tsarin Chiroptera. suna amfani da ƙwaƙƙwaran gabansu, wato gabobin su na farko a matsayin fuka-fuki, su ne kawai dabbobi masu shayarwa waɗanda ke shawagi mai dorewa. Jemage sun fi saurin tashi sama fiye da yawancin tsuntsaye, suna tashi da yatsun su masu tsayi da yalwa wanda suke lulluɓe da siraran nama.

Jemagu sun kasance a tsari na biyu mafi girma na dabbobi masu shayarwa bayan Beraye, sun kuma ƙunshi kusan kashi 20% na dukkan nau'ikan dabbobi masu shayarwa a duniya, fiye da nau'ikan 1,400. An raba waɗannan a gargajiyance zuwa gida biyu: Manyan-jemage (megabats) masu cin 'ya'yan itace da masu amfani da amsawar sauti domin gane inda abu yake wato Kananun-jemage (Microbats). Yawancin jemagu suna cin kwari ne, wasu kuma suna cin 'ya'yan itace ko furanni. kadan daga ciki ne suke cin wani abu daga dabbobi banda kwari; misali, jemage mai shan jini, wanda ya kasance yana tsutsar jini daga jikin dabbobi. Yawancin jemagu 'Yan-dare ne, kuma da yawa suna zama a cikin kogo ko wasu mafaka; Babu tabbas ko jemagu suna da waɗannan halayen domin tsira daga mafarauta. Jemage suna nan a duk faɗin duniya, ban da yankuna masu tsananin sanyi.


Amfanin Jemage

Jemage suna ba wa ɗan adam wasu fa'idodi kai tsaye, a farashin wasu rashin amfani. An haƙa kashin jemagu daga kogo kuma an yi amfani dashi azaman taki. Jemagu suna da muhimmanci a wurin auratayya tsakanin furanni da kuma yad'a iri; inda da yawa shuke-shuken da ke cikin Hamada sun dogara ga jemagu domin wannan aiki. Jemage na cinye kwari, wanda hakan yana rage buƙatar magungunan kashe qwari da sauran matakan sarrafa kwari. Koyaya de, wasu jemagu suma mafarauta ne na sauro, suna hana yaduwar cututtuka da sauro ke haifarwa. Masu noman 'ya'yan itace galibi suna ɗaukar jemagu a matsayin kwari masu 'barna. Saboda halittar jikinsu, jemagu nau’in dabba ne da ke aiki a matsayin ma'adanar cututtuka masu yawa, irin su ciwon Rabies; inda suke samun damar hakan, kasancewar suna da tafiye-tafiye, huld'ayya, da kuma tsawon rai, za su iya yada cuta a tsakanin junansu da sauri, huldar mutane da jemagu zata iya kasancewa mai hadari.


Ya danganta da al'ada, ana iya alakanta jemagu da abubuwa masu kyau, kamar kariya daga wasu cututtuka ko haɗari, sake haifuwa, ko tsawon rai, amma a yammaci, ana alakanta jemagu da duhu, lalata, maita, yan shan jini, da mutuwa.

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Read next

In 184 languages

haAfrikaansአማርኛaragonésÆngliscالعربيةمصرىঅসমীয়াasturianuAtikamekwKotavaAymar aruazərbaycancaتۆرکجهBasa Baližemaitėškaбеларуская (тарашкевіца)беларускаябългарскиবাংলাbrezhonegbosanskiбуряадcatalà閩東語 / Mìng-dĕ̤ng-ngṳ̄CebuanoTsetsêhestâheseکوردیcorsučeštinakaszëbscziчӑвашлаCymraegdanskdagbanliDeutschThuɔŋjäŋZazakiKadazandusunΕλληνικάemiliàn e rumagnòlEnglishEsperantoespañoleestieuskaraestremeñuفارسیsuomiNa Vosa Vakavitiføroysktfɔ̀ngbèfrançaisNordfriiskFryskGaeilge贛語GàidhliggalegoAvañe'ẽBahasa Hulontaloગુજરાતીwayuunaiki客家語 / Hak-kâ-ngîעבריתहिन्दीhrvatskiKreyòl ayisyenmagyarinterlinguaJaku IbanBahasa IndonesiaIdoíslenskaitaliano日本語JawaქართულიTaqbaylitKabɩyɛGĩkũyũқазақшаಕನ್ನಡ한국어перем комиکٲشُرkurdîkernowekкыргызчаLatinaLingua Franca NovaLimburgsLigureLadinlingálalietuviųlatgaļulatviešuMadhurâमैथिलीмокшеньMalagasyмакедонскиമലയാളംमराठीкырык марыBahasa Melayuမြန်မာဘာသာэрзяньمازِرونیNapulitanoNedersaksiesनेपालीनेपाल भाषाLi NihaNederlandsnorsk nynorsknorskNovialNouormandDiné bizaadoccitanlivvinkarjalaଓଡ଼ିଆиронਪੰਜਾਬੀKapampanganPicardpolskiPiemontèisپنجابیportuguêsRuna Simiikirundiromânăarmãneashtitarandíneрусскийрусиньскыйсаха тылаᱥᱟᱱᱛᱟᱲᱤsardusicilianuScotsسنڌيsrpskohrvatski / српскохрватскиTaclḥitSimple EnglishslovenčinaslovenščinachiShonaSoomaaligashqipсрпски / srpskiSeelterskSundasvenskaKiswahiliślůnskiSakizayaதமிழ்తెలుగుтоҷикӣไทยTagalogtoki ponaTürkçeئۇيغۇرچە / UyghurcheукраїнськаاردوTiếng ViệtWest-VlamswalonWinaray吴语хальмгייִדישYorùbáVahcuenghZeêuws閩南語 / Bân-lâm-gí粵語中文isiZulu

Text from Wikipedia, CC BY-SA 4.0 · Source article