Birnin Hague ( or 's-Gravenhage) shine babban birnin Holland ta Kudu na Masarautar Netherlands. Tana dauke da yawan al'umma fiye da rabin miliyan, Itace birni mafi girma ta uku a kasar Netherlands. Tana a gabar teku ta yamma tana kallon North Sea, Birnin Hague itace cibiyar gudanarwa ta kasar kuma a nana ne gidan gwamnati yake, amma duk da cewa babban birnin Netherlands da hukunce tana Birnin Amsterdam ne, Ana bayyana Birnin Hague a matsayin babban birni a baka tun lokacin Jahurriyar Dutch.
Hague ita ce babban gari na babban birnin Hague wanda ke dauke da mazauna sama da 800,000, kuma yana daga cikin yankin Babban Garin Rotterdam-The Hague, wanda, tare da yawan jama'a kusan miliyan 2.6, shine yanki mafi girma a Netherlands. Birnin kuma yana daga cikin yankin Randstad, daya daga cikin manyan birane a Turai.
Hague ita ce mazaunin majalisa, ministoci, Cibiyar jihohi, Kotun Koli, da Majalisar Jiha ta Netherlands. Sarki Willem-Alexander a hukumance yana zaune a cikin Huis ten Bosch kuma yana aiki a Fadar Noordeinde tare da Sarauniya Maxima. Yawancin ofisoshin jakadancin kasashen waje a cikin Netherlands suna nan a cikin birni. Har ila yau, Hague ita ce hedkwatar kamfanonin Holland da dama, tare da Shell plc da ke da manyan ofisoshi a cikin birni. Royal Library na KAsar Netherlands ma yana can. Yankin bakin teku na Hague ya haɗa da sanannen wurin shakatawa na bakin teku Scheveningen.
