

2 images
Maharashtra jiha ce, da ke a Yammacin ƙasar Indiya. Tana da yawan fili kimanin kilomita arabba’i 307,713 da yawan jama’a 112,374,333 (in ji ƙidayar shekarar 2011). Jihar tarayyar Indiya ce daga shekara ta 1960. Manyan biranen jihar su ne Mumbai ta Nagpur. Bhagat Singh Koshyari shi ne gwamnan jihar. Jihar Maharashtra tana da iyaka da jihohin biyar: Karnataka da Goa a Kudu, Telangana a Kudu maso Gabas, Chhattisgarh a Gabas, Gujarat da Madhya Pradesh a Arewa da Dadra da Nagar Haveli da Daman da Diu a Arewa maso Yamma.
Hotuna










11 images
