

2 images
Dominica ko Dominika (da Turanci: Commonwealth of Dominica; da Faransanci: Dominique; da harshen Karibiyan: Wai‘tu kubuli) ƙasa ce, da ke a nahiyar Amurka. Babban birnin ƙasar Dominika birnin Roseau ne. Dominika tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 750. Dominika tana kuma da yawan jama'a da suka Kai kimanin 71,625, bisa ga jimilla a shekarar 2018. Dominika tsibiri ne a cikin Tekun Karibiyan.
Daga shekara ta 2013, shugaban ƙasar Dominika Charles Savarin ce. Firaministan ƙasar Dominika Roosevelt Skerrit ne daga shekara ta 2004.wanda take da fadi a kalla 74656(2023).
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
