factograf
HA
Sign in

Chevron

Chevron
All data from the card 18
Suna a hukumance
Chevron
Iri
oil company (en) , enterprise (en) , public company (en) , gas station chain (en) , corporation (en) da ma'aikata
Masana'anta
petroleum industry (en)
Ƙasa
Tarayyar Amurka
Bangare na
Dow Jones Industrial Average (en) , S&P 500 (mul) , Seven Sisters (en) , Dow Jones Global Titans 50 (en) , list of companies involved in the Gaza war (en) da S&P 100 (mul)
Ƙaramar kamfani na
Texaco (mul) , Chevron (Canada) (en) , Chevron (Australia) (en) , Chevron (Netherlands) (en) da ExtraMile (en)
Ma'aikata
48,600 (2018)
Harshen amfani
Turanci
Kayayyaki
lithium grease (en)
Babban mai gudanarwa
Mike Wirth (en)
Shugaba
John S. Watson (en)
Tsari a hukumance
public company (en) da Business Corporation (mul)
Mamallaki na
Texaco (mul) , 1500 Louisiana Street (en) , Chevron Phillips Chemical (en) da Coalinga Solar Power Plant (en)
Haraji
202,792,000,000 $ (2024)
Net profit (en)
17,661,000,000 $ (2024)
Stock exchange (en)
New York Stock Exchange (mul)
Wanda yake bi
Standard Oil Company of California (en)
Awards received
Public Eye Environment Award (2006) : Lago Agrio oil field (en) Public Eye Lifetime Award (2015)
Stanley Park floating Chevron station
Stanley Park floating Chevron station
Matatar mai ta kamfanin a Kanada
Matatar mai ta kamfanin a Kanada
Wani gidan mai na Chevron a cikin Redwood City, California
Wani gidan mai na Chevron a cikin Redwood City, California
Matatar mai Mallakar kanfanin
Matatar mai Mallakar kanfanin
4 images

Kamfanin Chevron (NYSE) kamfanin sarrafa mai ne babba na ƙasashen duniya, tushen sa na can Ramon, California. An samar da kamfanin a shekarar 1984 kuma shi ne na uku a jerin manyan kamfononin man-fetur a Amurka. Yana ɗaukar sama da mutane dubu sitin 60,000 aiki. Yana ɗaya daga cikin manyan kamfanonin matatar mai guda shida a duniya.

Daga cikin harkokin kamfanin Chevron akwai hade-hade da sayar da hajojin man-fetur, maya-mayan inji, da sauran sinadarai da ake iya samu daga fetur. Wuraren da kamfanin tafi gudanar da harkokinta sun hada da yammacin gabar tekun Arewacin Amurka, Gulf Coast dake Amurka, Kudu-maso yammacin Asiya, Korea ta Kudu, da kasar Australia. A shekara ta 2018, kamfanin tana samar da akasarin barrel 791,000 a duk rana.

Tarihi

An kirkiri kamfanin Chevron a shekaran 1987, amma tarihin kamfanin ya fara tun watan Satumba na shekara 1879, lokacinda tsohon kamfanin na asali wato "Star Oil" ta soma hako mai a Filin-mai na Pico Canyon dake tsibirin Santo Susana dake arewacin Los Angeles a shekarar 1876, an ƙirƙiro Kamfanin Mai na Pacific Coast. Sun riƙe sunan har zuwa shekara ta 1906, lokacin da ta haɗu da wani kamfanin mai suna Standard Oil kuma ya zama Kamfanin Mai na (California). Standard Oil na California da Gulf Oil sun haɗu a cikin shekara ta 1984, wanda ya zama babbar haɗuwa a tarihi a wancan lokacin. Kamfanin zai canza sunansa zuwa Chevron Corporation a shekarar.

A watan Satumban shekarata 1879 Charles N Felton da Lloyd Tevis da George Looms da sauransu suka kirkiri Kamfanin "Pacific Oil Coast Company", wanda daga baya ta mamaye hannun jarrin " Star Oil" da jarin kudi dalala $1million.Man Kamfanin Pacific ya zamo mafi soyuwa a garin California daga baya kuma kamfanin "Standard Oil" ta siye ta akan kudi dala $761000 a 1900.Kamfanin Pacific ta ci gaba da gudanar da harkokinta na yau da kullum da sunanta har zuwa shekarar 1906, lokacin da aka hade ta da wani karamin kamfanin Standard Oil sai ya koma Standard Oil California ko California Standard.

Sai kuma mabiyinsa wato Texas Fuel Company wanda aka samat, a. Shekarar 1901 a garin. Beaumont dake Texas a matsayin dillalin kayan man-fetur wanda Bucksin ya samr. Kamfanin Texas Fuel sunyi aiki kusa da kusa da kamfanin Chevron. A shekarar 1936, kamfaninTexas sunyi hadin gwiwa da kamfanin Standard California don gina rijiyan mai a Saudiyya, wanda aka sanya wa inkiya da "Caltex".Texas Fuel Company ya koma Texas Company daga baya kuma Texaco.

A shekara ta 2000, kamfanin Chevron ta siya Texaco akan harkallan kudi dala Biliyan $45, wanda ya maida kamfanin na biyu a girma a duk fadin Amurka kuma na hudu a jerin manyan kamfanonin hada-hadan man fetur na duniya.

Jagoranchi

Micheal Wirth shi ne chairman kuma CEO na Kamfanin Chevron na yanzu

Sauran yanar gizo

Read next

In 59 languages

Text from Wikipedia, CC BY-SA 4.0 · Source article